Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A wani taron manema labarai gabanin ranar fasahar nukiliya ta kasa a Iran Islami ya ce "dukkan tuhume-tuhumen da ake yi kan samuwar wadannan wurare, sun samo asali ne daga zarge-zargen da yahudawan sahyoniya suka yi, wadanda ba su da tushe balantana makama."
Ya yi nuni da cewa nan ba da dadewa ba jami'an hukumar kula da makamashin nukiliyar za su ziyarci kasar Iran, inda ya kara da cewa Iran za ta sanya cikakkun bayanai kan shirinta na nukiliya a gaban jama'a da ma duniya baki daya, domin tabbatar da cewa zargin da ake yi bas hi da tushe.
Eslami ya kara da cewa: "Shirinmu na nukiliya na zaman lafiya ne, kuma bai sabawa ka'idojin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ba. Ba ma neman rikici da hukumar ta kasa da kasa, sai dai muna son mu'amala ta yau da kullum da ita, ba tare da siyasantar da batun ba."
Ya ce sakamakon binciken da hukumar makamashin nukiliyar ta gudanar ya zuwa yanzu ya dogara ne kan abin da ta gani kuma ta tabbatar, kuma wannan a cewarsa kokarin masanan Iran ne ba tare da taimakon wasu ba, kuma a karkashin takunkumin Amurka.
342/